Nigeria: Sifirin tumatir a kiret din roba na kara kwargon rayuwa—da kudin shiga na manoma

| April 16, 2020

Download this story

News Brief

A lokacin da Hajiya Tabawa Hamza take girbin tumatirin ta, ta loda su a cikin kiret na roba a maimakon kiret na gargajiya. Duk da cewa kiret din kanana ne, tafi son su akan, akan na gargajiya saboda tumatir kadan ne suke lalacewa a lokacin da ake sifirin su. Wanan yana nufin asara kadan. A dalilin haka, tana siyar da tumatir da yawa, sanan kudin da take samu ya nika na da sau biyar. Manoman tumatir da yawa a Jahar Kano dake Nijeriya na amfani da kiret na roba akan Kwando, Yanzu, tumatir kadan ne—da mutane—ke jin ciwo lokacin da ake sifiri.

A ranar Juma’a, wurin karfe shida na safe, Hajiya Tabawa Hamza ta gama girbin tumatirin ta kenan. Bazawara, mai shekaru tsaka tsaki, ta kwalla wa babbar yarta kira, ta ce mata tayi sauri ta dau tumatirin da ke cikin kiret din roba ta kai kasuwa.

Hajiya Tabawa ta zaune ne a karamar hukumar Bunkure dake kudun Jahar Kano a Nijeriya. Tana shuka tumatir ne a gona mai girman sukaya mita 100 da ta gada a wurin mijinta da ya mutu.

Hajiya na amfani da kiret din roba ne tayi sifirn tumatir zuwa kasuwa saboda tace yana karawa tumatirin ta kwargon rayuwa. Tana sanya tumatirin da tayi girbi a cikin kiret din roba tayi sifirin su zuwa garuruwa kamar Legas. Kiret din na taimakon tumatirin daka kurjewa, ko murkushewa, ko kuma lalacewa a lokacin da ake sifirin sa da jigilar sa.

Da tana sifirin sa ne kwandon saka da akayi da ganyen dabino da sanda, amma yanzu tafi san amfani da kiret.

Hajiya ta yi bayani: “A shekarun baya da suka wuce da kyar nake saida Kwando daya ko biyu a rana saboda lalacewa in ana sifirin sa acikin kwandon saka….yawanci masu wucewa daka cikin gari suke sunfi son sabin tumatir. Asara nakeyi kawai.”

Tana amfani da kiret din roba tun shekara ta 2018 kuma bata fuskantar matsalar lalacewa. Hajiya tace tana samun ciniki daka daka Kwando biyu zuwa kiret 10 ko 12. Wanan ya taimaka mata wurin samun kudin shiga daka Naira 6,000 ($16) zuwa Naira 30,000 ($81 US).

Kiret din tumatir yana da nauyin kilogiram 22. Kwandon tumatir kuma yana da nauyin kilogiram 60, saboda haka yana dauke da tumatir a kalla sama da kiret din roba biyu da rabi.

Mahmuda Dahiru shine shugaban manoma na Kwanar Gafan a karamar hukumar Bunkure, shima ya cenja da ka Kwando zuwa kiret din roba. A dalilin haka, mutumin dan shekara 57 yace, “Kudin shigowa ya karu daka Naira 33,000 ($89 US) zuwa Naira 44,000 ($119 US).”

Al Hassan Shugaba manomi ne a karamar hukumar Kura dake Jahar Kano. Shekara 25 yayi yana noma kuma yana kai tumatir Legas da sauran wurare masu nisa a Nijeriya. Shima yafi son amfani da kiret din roba yayi sifirin tumatirin sa.

Yace sanda yake sifiri da Kwando 100 na tumatir zuwa kasuwa daka gonar sa, yana asarar Kwando 10 zuwa 20 saboda lalacewa. Amma in yayi amfani da kiret din roba, kusan duka tumatirin suna zuwa inda ake so ba tare da sun lalace ba.

Malam Shugaba yace wani abun damuwa na amfani da Kwando shine ciwo da yake jiwa mutane da suke amfani dashi. Yace wani lokaci, daya da ka cikin mutanen da ya dauka suyi masa sifiri yaji ciwo a hannunsa da sai da aka kaishi asibiti saboda ya zuba da jinni sosai.

Mal Auwal Salisu shine mai gudanar da hadaka da hulda da yan kasuwa na Pyxera Global, wanda suke raba kiret din roba to kungiyoyin manoma. Yace amfani da kiret wurin sifiri yafi lafiya da arha, zai kuma taimakawa manoma su sami riba sosai saboda kara kargon rayuwa da yake na tumatir da kuma rage lalacewar tumatir.

Wanan binciken, an samar dashi ne daka tallafin Gidauniyar Rockefeller ta shirin su na Yieldwise initiative