Nijeriya: Warewa, Jerin-matsayi, da kuma kara daraja na karawa manoma kudin shiga

Download this story

News Brief

Mr. Obadiah na zaune a Jahar Plateau dake kasar Nijeriya a inda yake shuka dankalin dake samun ruwan sama a lokacin damuna da kuma noman dankalin ban ruwa a lokacin rani. Wanan yana bashi hanyar samun kudin shiga a shekara gaba daya. A yanzu haka, yana girnbin dankalin da ya shuka da rani yana kuma shirya gonar sa domin noman damuna. Mr. Obadiah na zaune a Jahar Plateau dake kasar Nijeriya a inda yake shuka dankalin dake samun ruwan sama a lokacin damuna da kuma noman dankalin ban ruwa a lokacin rani. Wanan yana bashi hanyar samun kudin shiga a shekara gaba daya. A yanzu haka, yana girnbin dankalin da ya shuka da rani yana kuma shirya gonar sa domin noman damuna.

A ranar Safiya ce mai dan sanyi, James Obadiah na tsaye a gonar dankalin sa, yana sha’awar yadda gonar dankalin sa tayi kyau tayi lafiya. Yace, “Na dade ina noman dankali kusan tsawon rayuwa ta saboda gado ne da na gada a wurin iyaye na.”

Mr. Obadiah na zaune a Jahar Plateau dake kasar Nijeriya a inda yake shuka dankalin dake samun ruwan sama a lokacin damuna da kuma noman dankalin ban ruwa a lokacin rani. Wanan yana bashi hanyar samun kudin shiga a shekara gaba daya. A yanzu haka, yana girnbin dankalin da ya shuka da rani yana kuma shirya gonar sa domin noman damuna.

Dankali na dauka sati 10 zuwa 12 kafin ya nuna haka kuma Mr. Obadiah na shuka irin dankali mai inganci kamar su konet, Nikola, F1, Marabel, da kuma Karuso.

Domin cimma amfanin gona mai albarka, da kuma gamsar da kasuwa sa, da kuma samun kudin shiga mai kyau, Mr. Obadiah na bin dokokin noma masu kyau kamar shirye-shiryen filin noma, cire ciyayi, shuka, girbi, rarabawa, jerawa da kuma karin daraja.

Yana raraba dankalin sa sau biyu zuwa uku kafin shuka, har da ma bayan girbi da kuma a wurin ajiya. Yana ware dankali na shuka da kuma na ci. Rarabawa na taimakawa Mr. Obadiah ya ware rubabu ko wanda suka kamu da cututka daka masu kyau, bayan haka ya binne wanda suka kamu da cututuka a wajen gonar sa.

Vou Shutt masanar Ilimin halittun shukoki ne dake Jami’ar Jos sashin Ilimin kimiyya da fasaha na Shukoki. Tace Rarabawa na da matukar amfani domin hana cututuka kama dankali masu koshin lafiya da kuma rage musu saurin tsiro.

Ms. Shutt tayi bayani cewa idan manoma suka shuka dankali mai dauke da cuta, ruwan sama na yada kwayoyin cutar ta cikin kasa zuwa sauran shukoki, wanda ke iya shafar gaba daya gonar.

Ta nemi manoma da sur araba danakalin su a ko da yaushe domin gudun asara. Tace: “Ku tabbatar kuna daukar dankalin shuka mai kyau zuwa gonar ka domin shuka. Idan kana da su masu kyau, toh kana da gona mai kyau mara cututuka. Wanan na tabbatar da cewa zaka samu amfanin gona mai kyau.”

Ms. Shutt ta kara da cewa manoma su guji amfani da yankaken dankali ko wanda yaji ciwo wurin shuka saboda suma na iya dauke da kwayoyin cututuka da kan iya kama sauran shukar. Tace mafita shine a raraba a cire dankali masu dauke da cuta lokacin girbi-kafin su watsa cututuka da kuma kwari kamar su bakteriya, kwarin asu da kuma burtuntuna lokacin ajiya.

Bayan girbi da wariya, manoma su jera dankali a bisa girman su. Emmanuel Shippi manomi ne dake karamar hukumar Pankshin a kasar Nijeriya. Yace jerin matsayi wana mataki ne da ya zama dole a wurin manoman dankalin.

Mr. Shippi yace: “Ina jera dankalin kasha uku a bisa girmansu: mafi kankanta, masu girman kwai, da kuma masu girman teburi. Masu girman kwai ina amfani dasu a iri, na teburin na siyarwa ne, mafi kanana kuma na iyali na ne domin cinsu dan suna dauke da sinadirai masu kyau.” Duk da duk dankali na dauke da sinadirai, mafi kananen sunfi sinadirai gina jiki domin basa dauke da sitaci mai yawa kamar manyan.

Manoman dankali a yankin na karawa noman daraja domin samun karin kudin shiga. Isaac Bawa manomi ne dake karamar hukumar Bokkos da yake karawa dankalin sa daraja bacin yayi jerin matsayi ta hanya sarafa shi zuwa garin dankali da kuma sitaci.

Mr. Obadiah yace warewa da jera dankali ya kara masa albarkar gona da kuma kudin shiga. Yace: “Irin dankali buhu day ana bani a kalla buhu hamsin na dankali bayan girbi. A kadada daya a kaka guda, ina girbin a kalla buhu 500 na dankali da nake sayarwa matsakaicin kudi Naira 12,000 zuwa 15,000 ($33-41 US) ko wana buhu mai nauyin kilogiram 50.” Dan haka kudin shigar say a kama Naira 6,000,000 zuwa 7,500,000 (16,320-20,400 US) —kudi shiga mai kyau na kokarin sa.

Wanan aikin an dauki gudanar dashi ne daka gudumuwar kudi da “Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH” (GIZ) ya bayar, wanda suke gudanar da cibiyar “Green Innovation” tare da hadin gwiwar AFC Agriculture and Finance Consultants.