Nigeria: Manoma a Nijeriya sun dauki shawarwarin aiki na kula da cutar dake kama tsiran dankalin turawa

| March 17, 2020

Download this story

News Brief

In Plateau State, Nigeria, the first rains signal the start of the planting season, but also the time that late blight can infect Irish potatoes. Farmers are being advised to use a variety of good practices and quality, disease-free, certified planting materials to reduce the risk of late blight. But certified seeds are expensive and scarce—Mary Bwakat has never had an opportunity to use them. Instead, many farmers rely on proper spraying practices and positive selection, which means only selecting healthy plants to be harvested and cultivated. Other recommended practices include crop rotation and sole cropping.

Ruwan farko na damuna shine ke nunawa cewa shuka bana ya kama. Tana sanye da zani mai ruwan kasa da kuma riga mai ruwan yalo, Mary Bwakat ta riga ta shiga gona dan share filin ta da niyar shuka dankali.

Tana murna da zuwan ruwan sama amma kuma tana da dan damuwa a ranta. Ta damu cewa cututuka daka zuwa lokacin damuna-kamar cutar tsirai-na iya kai wa shukar ta hari.

Cutar tsirai na iya ruguje albarka shukar dankali. Mrs. Bwakat ta ce, dan suyi maganin cutar, ana bawa manoma shawara amfani da iri mai kyau, mara cututaka, wanda kuma aka yadda dashi tare da aikata ire-iren noma na gari. Amma, iri mara sa cututuka na da tsada kuma na da wuyar samu.

Tace, “sama da shekara 15 ina noman dankali, amma ban taba gani ko amfani da iri mai kyau, wanda kuma aka yarda da ingancin sa ba.”

Mrs. Bwakat ta na zaune a kauyen Maikatako a karamar hukumar Bokkos dake Jahar Plateau a yankin arewa ta tsakiya a kasar Nijeriya. Jahar Plateau ce matatarar noman dankalin turawa a kasar, ana kuma sifirin shi zuwa wurare da yawa. Wanan yana nufin, dankalin turawa na daya daka cikin muhimman hanyar samun kudin shigowa ga manoman kauyukan.

Duk da cewa yanayin Jahar Plateau yasa noman dankali na da tasiri, akwai raraguwa noman dankali saboda cutar dake kama tsirai.

Micah Bature, mai shekaru 68 yana noman dankalin turawa sama da shekaru 30 a Jahar Plateau. Ya yadda cewa iri mai kyau da ka yadda da inganci shi, na da wuyar samu a wurin kananen manoma. Amma, shi da sauran manoma irinsa na samun nasara wurin amfani da salo daban-daban dan kariya daka cutar tsirai.

Danbaba Anthony shine mai lura da bangaren dankalin dake karkashin cibiyar National Root Crop and Research Institute a Jahar Plateau. Cibiyar tasu nayi bincike dan inganta noma, sarafawa da kuma ajiyar tushe na amfanin gona. Mr. Anthony ya bawa manoma shawara da suna amfani da hanyoyin feshi da suka dace da kuma zabi da ya dace; hanyar da manoma ke girbe shukoki masu lafiya.

Shippi Emmanuel shine ciyama din kungiyar yan kasuwan dankali da kayan lambu ta Solanum. Yace manoma dake bin hanyoyi nom ana kwarai sun dena tosron cutar tsirai kana kuma suna samun karuwa wurin noma.

Mr. Emmanuel ya lissafa salo kala-kala na noma da zai taimaki manoma su samu amfani gona masu lafiya ya basu kuma riba. Wanan sun hada da juya shuka, noman shuka guda, yin amfani da maganin kwari, sanan da zabar shukoki masu lafiya wurin noman shekara mai zuwa, bayan sati sida zuwa takwas da shuka.

Dawam Jonathan shima na noman dankalin turawa a Jahar Plateau. Yace, “Ina amfani da salon juya shuka, zabi mai kyau, da kuma amfani da maganin kwari da maganin funfuna dan kariya daka cutar tsirai.

Mrs. Bwakat tace noma na kwarai ya taimaka mata maganin cutar digon baki ya kuma bunkasa mata amfanin gona da ya kara mata samun kudin shiga. Tana samun a kalla 250,000 Naira kudin Nijeriya ($615 US) akan Naira 100,000 zuwa 120,000 kudin Nijeriya ($245 zuwa $295 US) da take samu a baya

Tace: “Da nake samun kudin shigowa masu yawa…ina iya tara kudin makarantar yara sanan in samu kudin abun yi a gida.

Wanan aikin an dauki gudanar dashi ne daka gudumuwar kudi da “Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH” (GIZ) ya bayar, wanda suke gudanar da cibiyar “Green Innovation” tare da hadin gwiwar AFC Agriculture and Finance Consultants.