Nijeriya: Hakkin kula da gida— shin nauyi na kan mata ne ko kuma aikin hadaka ne?

| June 7, 2024

Download this story

News Brief

Margaret Oraza ma’aikaciyar gwamnati ce kuma uwa ce da take da yaya biyar, ta na zaune a garin Makurdi dake kasar Nijeriya, a kullum tana fama da yada zata daidaita aikin ta na gwamnati da kuma sauran ayyukan gida. Halin da take ciki na kara jadada irin manyan alamuran da ke tatare da matsayin jinsi acikin aikace-aikacen gida. Cecilia Madu, kwarariya akan nazarin jinsi, ta ce dole ne al'umma su yi koakarin raba ayyukan gida tsakanin maza da mata, sanan su san muhimancin gudunuwar da mata suke bayar wurin tafiyar da gida. Wanan yunkurin cenjin da ake son kawo wa, zai magance irin kallon da ake yiwa mata cewa aikin gida na sune, sanan ya kara ingancin daidaito acikin gidajen mu.

A kowace safiya cikin makon Febweru, Margaret Oraza tana tashi karfe 4:30 na safe, dan tafara aikin gida kafin ta tafi aiki, duk da duhun dare da kuma iskar sanyin da take hurawa a irin wanan lokacin. Uwar yaya biyar yar shekara 41, tana tafasa ruwan zafi akan gawayi dan iyalinta suyi wanka idan sun tashi. Sanan ta fara hada musu abun karyawa. Aikace-aikacen safe da takeyi ya na daukar kusan awa hudu. Tace, “wani lokacin, aikin da nakeyi a gida ya na da illa akan aikin da nakeyi in naje opis, saboda gajiya da wahala.”

Misis Oraza maaikaciyar gwamnati ce dake aiki a Ma’aikatar yada labarai, al’adu, da yawan bude ido. Tana zaune tare da mijinta da yayansu biyar a Wurukum, Makurdi, da take jahar Benue a kasa Nijeriya. Taimakon da take samu daka mijinta dan kadan ne saboda rashin lafiya da yake fama da ita. Bemgba Oraza na da ciwon hawan jini da siga.

Duk da dai Misis Oraza tana aiki sosai, yayan ta na bada taimako suma wurin taimaka mata da aikin gida kamar, daka yaji, wanke-wanke, debo ruwa da kuma sauran aike. Baban danta, mai shekaru 19, na karatun digiri a fanin anatomy a jami’ar jahar, ya na kuma yin leburanci. Yana yawan ba wa mahaifiyar sa kyautan kudi, ya na kuma rokon mahaifin sa da ya na daurewa yana taimakawa wa mahaifiyar sa da wasu aiyukan gida dan ya saukaka mata nauyin da ke kanta. Yayan Misis Oraza na ganin darajar ayyukan da ta keyi a gida da kuma irin taimakon kudi da take bawa gidan gaba daya.

Amma, Misis Oraza ta kara bayani da: “Mijina da yaya nan a da iyaka akan abun da zasu iya taimako na dashi. Da yawan lokuta, ni nake karasa ayyukan yau da kullum a gida, kamar in faskaren itace, dakan doya, wanda wanan ya na samun gajiya da yawan jin yunwa.”

Misis Oraza, ta yarda alumma na hakkin fadawa mazaje masu aure su na taimakawa matayen su a gida saboda kar su zama cikin gajiya ko yause. Ta ce, “maza su daina kallon matan su a matsayin bayinsu, illa a matsayin mataimakan su.” 

Cecelia Madu ma’aikaciyar kulawa da jin dadin jama’a ce da take wacce ke aiki a matsayin jami’ar horo da bincike a cibiyar nazarin jinsi a jami’ar jihar Benue da ke Makurdi. Ta ce, duk da cewa mata na iya ayyuka da yawa a lokaci daya, akwai bukatar a ba wa maza da mata dama iri daya a gida. 

Malama Madu ta yi imanin cewa ko dai a biya mata albashin aikin da suke yi a gida, ko kuma maza su fahimci bukatar taimakawa da ayyukan gida. Ta kara da cewa, “rawar da mata ke takawa a gida na da kima sosai. Da akwai bukatar maza su san muhimancin wanan gudunmuwar da mata ke bayar wa, sanan su zama ma su nuna godiyar su ga lokaci, da karfin jiki, da mata suke saw a wurin tafiyar da alamuran gida.”

Malama Madu tana kira ga alumma da su sauya tunanin su na da yake ware “aikin mata” daban “aikin maza” daban. Ta ce wadanan sunaye da ake bawa ayyukan maza daban da ayyukan mata daban ba wai kawai yana dakile cigaba bane, amma suna kara karfafa ra’ayoyi ma rasa tasiri, wanda zai iya wa duka jinsin illa. Ta kara da cewa kowa zai iya yin kowane aiki, Malama Madu ta kara haske akan wayar da kan mutane da kuma hadin kai wurin daidaita damar samun aiki ga kowa. Ta yi kira da a sake duba kan ayyuka, da yadda ko wana gida ke daukar muhimancin aikin, ta bukaci a tabatar da cewa ana kula da daidaito da adalci wurin daukar aiki.

Emmanuel Onah, shine mataimakin direkta a Ma’aikatar jaha dake Benue, matar sa kuma koyarwa take jami’ar da ke jahar. Suna da yaya biyu, kuma tuni sun koyi raba aikin gida daidai da daidai a tsaknain su.

Mista Onah yace saboda muna raba aiki, akwai danko mai karfi domin cigaban gidan mu. Yayan su ne suke goge-gogen gida da wanke-wanke, ita kuma matar sa ta dafa abinci, da taimakon sa da na yaran sa. 

Ya ce, da yake matar sa na da aiki da yawa a opis, ta na bukatar duk taimakon da za ta samu. Ya dada da cewa, “ina jin dadin taimakawa da ayyuka a gida na, wana sai ya ke sa wa ina jin sauke wani hakki da ba da gudunmuwa ta.”

Mista Onah ya cigaba da cewa: “da nishadi, nake taimakawa da ayyukan gida kamar yiwa yaro na dan shekara takwas wanka sanan in shirya shi ya tafi makaranta. Ina zuwa kasuwa itama, kai yara makaranta da kuma yin wanki da guga.”

Matar Onah tace ta na jin dadin taimakon da take samu da ka mijin ta da yayan ta, wanda ya ke taimakawa wurin rage ma ta damuwa da wahalar aiki da kuma sauran ayyukan gida. Ya na kuma bata lokaci ta samu tayi wasu abubuwan a hutun karshen sati. Matar Onah ta rufe da cewa, “Ina godiya da taimakon da nake samu da ka iyali na.”

An samar da wanan ne ta shirin ‘UCARE – Unpaid Care in sub-Saharan Africa‘, wanda ke da kudirin habaka daidaiton jinsi da kuma karfafa mata ta hanayar jadada yin adalci da daidaito wurin raba ayyukan kulawa da ba’a biya da ayukan gida a tsaknin duk mazauna cikin gida a nahiyar kuda da hamadar Afrika. An aiwatar da aikin ne da ahdin gwiwar gidan Farm Radio International (FRI), UN ta Mata, da kuma cibiyar sadarwa da cigaban mata ta Afrika (FEMNET) godiay mai yawa da tallafin Global Affairs Canada.