Nigeria: Manoman Tumatir na gudun cinkoson kasuwa ta hanyar tsagaita shuka

| April 16, 2020

Download this story

News Brief

Jibril Sule Dakasoye na noma a gona da girman ta yakai kadada daya—da—rabi a kauyen Kawma, kusa da garin Kano a tsakiyar Nijeriya. Yana shuka tumatir da sauran kayan lambu, amma yana yi a hankali dan ya tsagaita shuka tumatirin sa. Yana raba gonar tumatirin sa gida hudu ya kuma shuka ko wane bangare daban-daban bayan sati uku. Wanan yana taimaka masa wurin girbin tumatirin sa da sayar da su a lokaci daya. Sakamakon shine farashi mai kyau na tumatirin sa, saboda ya guji cunkoso a kasuwa yayin da tumatirin manoma da yawa suke kasuwa a lokaci daya.

Ranar, lahadi ce da safe, amma Jibril Sule Dakasoye na hanyar sa ta zuwa gona. Yana tuka tsohon kekensa da kacha sa ke kara. Yana dagawa mutane hannu yayin da yake wuce su zuwa gona dan ya hadu da yayansa.

Malam Sule yace ba ya iya taimakawa yaran sa a da saboda yawan tumatir a kasuwa na kawo arha farashi. Domin shawo kan wanan kalubale, sai yake tsagaita shuka tumatir domin gudun girbi da sayar da tumatirin sa a lokaci daya. Yace, “Bana saurin kai tumatiri na kasuwa.”

Malam Sule, wanda shekarun sa sun kai 40 da dori, yana zaune ne a kauyen Gawma, kilomita 75 daka cikin garin Kano a kasar Nijeriya. Ya fara noma shekaru 28 da suka wuce yana da kuma gona mai girma hekta daya-da-rabi. Bayan tumatir, yana noman masara, kokumba, kabeji da kuma kayan lambu.

Wanan yana bashi hanyoyi samun kudin shiga da yawa. Idan farashin tumatir baiyi masa ba, sai ya siyar da kukumba da yalo. Da ace noman tumatir yake kawai, yace wanan dabara da yayi yasa baya fargaba samun kudin shigowa ko da farashi a kasuwa zai cenja.

Tsagaita shuka da yakeyi yasa Malam Sule yake zaba farashin da yayi masa, ya kuma samu kudi da yawa daka saida tumatir. Domin ya samu saukin tsagaita shukar sa, sai ya raba gonar sa gida hudu yayi shuka a kowana bangare sati uku a Tsakani. Wanan ya taimaka masa wurin kaucewa girbi da sayar da tumatirin sa a lokaci daya.

Shekaru 14 da suka wuce, Malam Sule da sauran manoma a unguwarsu suka samu labarin tsagaita shuka daka gwamnatin tarayya a wani shirin su na manoma da ya bada muhimmanci a wuraren bakin ruwa. Yace kafin ya fara tsagaita shuka, masu siye na amfani da cinkosan kasuwa suna yiwa manoma tayin wulakanci da kuma kin yadda ayi amfani da sikeli a auna tumatirin.

Yayi bayani: “Saboda manoma nayin shuka da girbi a lokaci daya, masu siye na zuwa da kwandon su na daban, wanda yafi namu girma. Kuma haka muke siyar musu dashi da yawa a kudi kadan, muyi ta asara.”

Allahasan Shugaba na shuka da siyar da tumatir a karamar hukumar Kura dake Jahar Kano. Mallam Alhassan yace cinkoson kasuwa na faruwa ne yayin da manoma ke saurin shuka tumatir a lokacin da ruwa yake a saukake.

Adamu Usman manomi ne a Garun Mallam da yake tallafawa yayansa 19 da matayen sa daka kudin da yake samu daka tumatir. Yace, “Na koyi ilimin tsagaita shuka. Ya kuma taimake ni sosai wurin inganta shukata da girbi duk bayan sati.”

Ya kara da cewa, “Ina gudun cinkoson kasuwa ta hanyar kiran waya inji ya kasuwar take da kuma farashi a lokacin kafin nayi girbin tumatiri na.”

Dahiru Mukhtar masanin kasuwancin gona ne kuma mai bada shawara ne a bangaren kasuwanci a Technoserve dake Jahar Kano. Kungiyar mai zaman kanta na aiki da manoma ne dan gina gonake masu takara da juna.

Mallam Mukhtar yace: “Idan akwai karancin tumatir a kasuwa, manoma sunfi samun kudi. Idan kuma yayi yawa, farashi yana yin kasa. Manoma zasu fi samun kudin shiga idan suka bi hanyar tsagaita shuka mai kyau.”

Mallam Sule yayi murna cewa tsagaita shuka tumatir da yake ya janyo masa karin samun kudin shiga, Yanzu yana iya taimakon matarsa da yayan sa 14. Yace, “Tunda na fara tsagaita shuka da kuma binciken yanayin kasuwa, samun kudi nay a karu daka sayar da tumatir. Yanzu har kudin kashewa nake baiwa yara na a duk wata.”

Wanan binciken, an samar dashi ne daka tallafin Gidauniyar Rockefeller ta shirin su na Yieldwise initiative